Bangaren kasa da kasa: Shugaban bangaren al'adu na jaridar Gilan Posten ta kasar Danmark da ta watsa zane-zanen batunci ga manzon Allah (SAW) a shekara ta 2005, ya bayyana cewa mabiya addinin musulunci ba su barin ko ta kwana a duk lokacin da aka taba addininsu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa a wata zantawa da ta hada shi da wata jaridar Haramtacciyar Kasar Isra'ila a wata ziyara da yake kaiwa a birnin Telviv Shugaban bangaren al'adu na jaridar Gilan Posten ta kasar Danmark da ta watsa zane-zanen batunci ga manzon Allah (SAW) a shekara ta 2005, ya bayyana cewa mabiya addinin musulunci ba su barin ko ta kwana a duk lokacin da aka taba addininsu. Felmin Zer ya bayyana hakan ne sakamakon martanin da jaridar ta fukanta bayan da ta buga tare da zane-zanen batunci ga manzon Allah a cikin shekara ta 2005, inda musulmin duniya ga baki daya suka mayar da martini kan hakan, duk da cewa mahukuntan kasar Danmark sun yi kunnen uwar shegu da kraye-kirayen musulmi suka yi na a ladabtar da jaridar, amma hakan ya yi tasiri wajen nuna waduniya matsayin manzon Allah SAW a jane al'ummar musulmi.
392850