Bangaren kasa da kasa: Saboda irin cikakken goyon bayan da Haramtacciyar Kasar Isra'ila take samu daga manyan kasashen duniya ne take yin hawan kawara a kan dokoki na kasa da kasa ba tare da an iya gurfanar da ita ba, kamar yadda ba za a iya bincika ayyukan ta'addancin ba ko yin Allawadai ita.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; alkalin alkalan kasar Malazia Zaki Azmi ya bayyana cewa; Saboda irin cikakken goyon bayan da Haramtacciyar Kasar Isra'ila take samu daga manyan kasashen duniya ne take yin hawan kawara a kan dokoki na kasa da kasa ba tare da an iya gurfanar da ita ba, kamar yadda ba za a iya bincika ayyukan ta'addancin ba ko yin Allawadai ita. Alkalin alkalan kasa ta Malazia ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da ake gudanar da taron alkalan kasashen musulmi a birnin Tehran, dangane da yadda ya kamata su dauki matakai na shari'a domin gurfanar da Isra'ila a gaban kuliya kan laifukan yaki da ta tafka a kan al'ummar Gaza. Ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai kararraki 153 da aka shirya gabatarwa kan ayyukan yaki da Isra'ila ta aikata kan al'ummar Gaza, kuma tuni aka mika su ga kotun manyan laifuka ta duniya.
392472