Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; kungiyar kula harkokin ilimi da al'adun musulunci ta ISESCO zata halarci taron kasa da kasa kan ilmi da kuma harkokin zamantakewa da za a gudanar a birnin Bargamo na kasar Italia. Bangaren yada labarai na kungiyar ne ya sanar da hakan a jiya. Babbar manufar gudanar da wannan taro dai ita ce kara karfafa ayyukan hadin gwiwa tsakanin asusun tallafawa kananan yara da mata na UNESCO da kuma jami'oi ta fuskacin kula da ilmin kanan yara a duniya, musamman ma a kasashe masu rauni. Jami'ar kasa da kasa ta Bargamu ce ta kasar Italia za ta dauki nauyin bakuncin taron, wanda zai samu halartar masana daga kasashen duniya daban-daban, daga ciki kuwa har na larabawa da musulmi.
392714