Bangaren fasaha: Salon rubutun Iraniyawa ya samo asali ne daga kur'ani, kamar yadda akasarin rubuce-rubucen Iraniya suke dauke da ayoyin kur'ani mai tsarki tun zamun da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga cibiyar adana kayan tarihi ta kasar Iran cewa; salon rubutun Iraniyawa ya samo asali ne daga kur'ani, kamar yadda akasarin rubuce-rubucen Iraniyawa suke dauke da ayoyin kur'ani mai tsarki tun zamun da suka gabata. Babban jami'i mai kula da cibiyar ya bayyana cewa yanzu haka akwai wasu kayan tarihi da aka ajiye su a cibiyar, wadanda tarihinsu yake komawa ga shekaru sama da dubu daya da wasu daruruwa, da ke bayyana yadda rubutun iraniyawa da suka fi shahara da shi ya samo asali daga rubutun kur'ani, wanda hakan ya hada da rubutun ayoyin kur'ani da aka rubuta kan wasu fatu, ko sassaken itace da dai sauransu, wanda hakan ke danganta asalin rubutun da kur'ani mai tsarki.
392396