Bangaren zamantakewa: Za a gudanar da wani taron karawa juna sani kan muhimman abubuwan da ya kamata ma'aurata su sani tare da kiyaye su kafin su yi aure.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen lardin Ahvaz ya habarata cewa; za a gudanar da wani taron karawa juna sani kan muhimman abubuwan da ya kamata ma'aurata su sani tare da kiyaye su kafin su yi aure. Rahoton ya ci gaba da cewa daliban jami'ar Azad ta birnin Ahvaz ne suka shirya gudanar da taron, wanda zai samu halartar takwarorinsu dalibai daga wasu jami'oi na kasar Iran, kamar yadda taron zai samu halartar wasu daga cikin malaman addinin musulunci na kasar, da kuma wasu malaman jami'a. Wakilin jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran da ke lardin shi ne zai jagoranci bude taron na yini guda. Yanzu haka malamai da suka gabatar da jawabai sun shirya makaloli da za a raba awajen taron.
390214