Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Mnasun Hakikatpoor gwamnan lardin Ardabil ya bayyana cewa; suna nan suna kokarin samara da hanyar sufurin jiragen sama daga bienin Ardabil zuwa birnin Najaful ashraf na kasar Iraki. Gwamnan na Ardabil ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gudanar da wani zama tare da jami'an hukumar kula da harkokin sufuri ta lardi, inda ya jaddada cewa daya daga cikin muhimman abubuwan da suke su aiwatar cikin 'yan lokutan nan shi ne, samara da hanyar sufuri ta jirgin sama daga lardin zuwa birnin najaf, bisa la'akari da yawan ziyara da mutanen lardin suke kaiwa wurare masu tsarki da ke kasar Iraki. Ya ce ko shakka babu samara da wannan hanya zai taimaka wajen cimma wannan buri.
392275