Bangaren al'adu da fasaha: Majalisar Dinkin Duniya ta zabi birnin Beirut a matsayin cibiyar littafi ta duniya a shekara ta 2009, bisa rawar da Labanan ta taka wajen kara kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai, musamman ma mabiya addinan kiristanci da na musulunci, tare da zama lafiya da juna.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Labanan ya habarta cewa; Majalisar Dinkin Duniya ta zabi birnin Beirut a matsayin cibiyar littafi ta duniya a shekara ta 2009, bisa rawar da Labanan ta taka wajen kara kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai, musamman ma mabiya addinan kiristanci da na musulunci, tare da zama lafiya da juna. A cikin wani bayani da majalisar dinkin duniya ta fitar jiya an bayyana cewa birnin Beirut shi ne ya buga littafai fiye da kowane a birnin a cikin 'yan lokutan nan kan kusanto da fahimta tsakanin mabiya addinai tare da zaman lafiya a tsakaninsu. An kirkiro bayar da kyauta ga biranen da suka fi taka rawa wajen yawan rubuce-rubuce tun a cikin shekara ta 1996, yayin da birnin Madrid na kasar Spain ya samu wannan kyauta a cikin shekara ta 2001 ya samu wannan kyauta.
391839