IQNA

Kafofin Yada Labaran Makiya Na Nufin Kawo Cikas Ga Tsarin Musulunci

14:01 - April 23, 2009
Lambar Labari: 1768807
Bangaren rahoto: Babban daraktan cibiyar yada al'adun musulunci reshen lardin Khorasan, ya bayyana cewa babbar manufar makiya wajen yada parpagandar karya kan addinin musulunci, ba wani abu ba ne illa kokarin bata surar tsarin musulunci a idon duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Zainul Abidin Rohani Niya babban daraktan cibiyar yada al'adun musulunci reshen lardin Khorasan, ya bayyana cewa babbar manufar makiya wajen yada parpagandar karya kan addinin musulunci, ba wani abu ba ne illa kokarin bata surar tsarin musulunci a idon duniya. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yke zantawa tare da shugaban muryar jamhuriyar musulunci reshen lardin Khorasan. Ya ci gaba da cewa ya zama kafofin yada labarai na cikin gida da ma wadanda suke yada shirye-shiryensu zuwa kasashen ketare, da su mayar da hankali wajen kara fadakar da mutane dangane da shirin makiya na bata surar juyin juya halin musulunci, da kuma tsarin da ke tafiyar da shi.

392215




captcha