Bangaren siyasa: Mataimakin shugaban majalisar shawara ta kasar Iran ya bayyana cewa; matsayin da gwamnatin Iran ta dauka dangane da zaman yaki da nuna wariya da majalisar dinkin duniya ta shirya a birnin Geneva na kasar Switzerland, da aka ba taken Durban na biyu, ya rikita siyasar Isra'ila a nahiyar turai
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wani zama da jalisar shawara ta Iran ta gudanar jiya mataimakin shugaban majalisar shawara ta kasar Iran ya bayyana cewa; matsayin da gwamnatin Iran ta dauka dangane da zaman yaki da nuna wariya da majalisar dinkin duniya ta shirya a birnin Geneva na kasar Switzerland, da aka ba taken Durban na biyu, ya rikita siyasar Isra'ila a nahiyar turai. Ya ci gaba da cewa shugaban kasar Iran mahmud Ahmadinejad, ya yi bayanai masu matukar tasiri a wajen taron, inda ya bayyana Haramtacciyar Kasar Isra'ila a matsayin wata daula da aka kafa kan nuna wariya tare da danne hakkokin al'ummar palastinu. Sama da kungiyoyin farar hula 4000 ne suka hakarci taron daga kasashe-daban-daban na duniya, domin nuna rashin amincewarsu da tsarin zxalunci da danniya da ke mulki da duniya.
392176