Bangaren internet: An bude wani sabon shafin internet dangane da taken da jagoran juyin juya hali na kasar ya baiwa wanna sabuwar shekara ta Iraniyawa, da ke nufin yin tattali da rage almubazzaranci a cikin harkokin yau da kullum da ayyukan gwamnati, wanda hukumar radiyo da talabijin din Iran ta dauki nauyin budewa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; an bude wani sabon shafin internet dangane da taken da jagoran juyin juya hali na kasar ya baiwa wanna sabuwar shekara ta Iraniyawa, da ke nufin yin tattali da rage almubazzaranci a cikin harkokin yau da kullum da ayyukan gwamnati, wanda hukumar radiyo da talabijin din Iran ta dauki nauyin budewa. An bude shafin ne da nufin yin Karin haske dangane da manufar baiwa wannan shekara wanna take, tare da kawo bayanai kan mahangar Imam Khomeini (RA) dangane da muhimmancin da ke tattare da kiyaye tsari, da kuma yin tattali a cikin lamurra da rage almubazzaranci, gami da hadisai na Manzon Allah da kuma limaman gidansa dan gane da hakan.
392159