Kamfanin dillancin labaran ikna ya habarta cewa, sa'id Mortazavi babban alkalin kotun birnin Tehran ya bayyana cewa zaman alkalan kasashen musulmi da aka bude a birnin Tehran ba zai kasa a gwiwa wajen wajen daukar matakan da suka dace domin fuskantar ta'addancin Haramtcciyar Kasar Isra'ila.Ya kuma bayyana hakan ne a jiya a lokacin da aka bude zaman taron na alkalan kasashen musulmi a birnin Tehran, da nufin yin dubi kan matakan shari'a day a kamata alkalai da kungiyoyin lauyoyi na kasashen musulmi su dauka domin kalubalantar Haramtacciyar Kasar Isra'ila kan ayyukan ta'addanci da take aikatawa kan al'ummar palastinu, da kuma barazanar share dukkanin lamomi masu daraja na al'ummar musulmi da ke cikin yankunan palastinawa da ta mamaye, masallacin Qods mai alfarma na daya daga cikin wurare masu tsarki da ke fuskantar barazanar rushewa daga yahudawan sahyuniya.
392168