Bangaren kasa da kasa: Cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta birnin Dubai ta shirya gudanar da wata gasar hardar kur'ani ta matasa, da aka yi wa take da cewa, da kura'ni nake rayuwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Wam na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa cewa; Cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta birnin Dubai ta shirya gudanar da wata gasar hardar kur'ani ta matasa, da aka yi wa take da cewa, da kura'ni nake rayuwa. Jami'ar da ke kula da harkokin cibiyar A'isha Alkas ta bayyana cewa; babbar manufar gudanar da wannan gasa ita ce karfafa gwiwar matasa wajen samun masaniya dangane da addinin musulunci, tare da kara zaburar da su zuwa ga karatun kur'ani da kuma hardarsa. An gudanar gasar ne a birnin Dubai, inda yara gami da matasa 142 suka shiga cikin gasar. Za a ci gaba da gudanar da irin wannan gasa duk bayan watanni tare da kara yawan masu shiga cikin gasar.
393633