IQNA

Kare Al'ummar Gaza Bai Kebanci Musulmi Ba Kawai

15:18 - April 25, 2009
Lambar Labari: 1769249
Bangaren kasa da kasa: Ayyukan ta'addancin da ake aikata wa kan al'ummar Gaza ana aikata sun e kan 'yan adamtaka, saboda haka kare hakkin mutanen da ake zalunta a Gaza ba hakki ne kawai day a rataya kan musulmi ba, hakan hakki ne day a rataya kan dukkanin al'ummomin duniya.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da wani daya daga cikin alkalai kuma mamba a kungiyar alkalai na kasa da kasa, wanda ya samu halartar taron alakalan kasashen musulmi da aka gudanar a birnin Tehran, domin daukar matakan shari'a da suka kamata domin gurfanar da Haramtacciyar Kasar isra'ila a gaban kuliya kan ayyukan yaki da ta tafka kan al'ummar palastinu, ya bayyana cewa Ayyukan ta'addancin da ake aikata wa kan al'ummar Gaza ana aikata sun e kan 'yan adamtaka, saboda haka kare hakkin mutanen da ake zalunta a Gaza ba hakki ne kawai day a rataya kan musulmi ba, hakan hakki ne day a rataya kan dukkanin al'ummomin duniya. Ya ci gaba da cewa dukkanin al'ummomin duniya sun ga hakikanin cin zarafin dan adam a Gaza, wanda kuma mafi yawan al'ummomin duniya musamman ma masu lamiri daga cikinsu sun yi Allawadai da hakan, a kan haka nauyin day a rataya kan al'ummomin duniya bai tsaya ga yin Allawadai ba, hakkinsu ne su kare al'ummar Gaza tare da ba su dukkanin taimakon day a kamata.

393557
captcha