IQNA

Kasashen Musulmi Na Taka Rawa Wajen Tabbatar Da Sulhu A Duniya

15:17 - April 25, 2009
Lambar Labari: 1769250
Bangaren kasa da kasa: Alkalin alkalan kasar Senegal ya bayyana cewa kasashen musulmi suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sulhu da zaman lafiya a sassa daban-daban na duniya, amma ya kamata su aiwatar da babban aikin da ke gabansu na taimaka ma al'ummar palastinu.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da alkalin alkalan kasar Senegan Madike Niang, ya bayyana cewa kasashen musulmi suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sulhu da zaman lafiya a sassa daban-daban na duniya, amma ya kamata su aiwatar da babban aikin da ke gabansu na taimaka ma al'ummar palastinu. Ya ci gaba da cewa bisa la'akari da halin da a l'ummar palastinu suke ciki a halin yanzu sun e suka fi bukatuwa ga duk wani kokarin tabbatar da sulhu da zaman lafiya da kasashen musulmi suke gudanarwa a wasu kasashe na daban. Ya ce ya zama wajibi a yaba wa Iran kasantuwar kasar musulmi da ke taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da taruka na haka kan kasashen muslmi domin fukantar abin da ked a muhimmanci a wurinsu, musamman ma batun palstinu.

393591
captcha