Bangaren kasa da kasa: Babbar matasalar da ake fuskanta wajen gurfanar da Haramtacciyar Kasar Isra'ila a gaban kuliya ita ce hawa kujerar naki da kasashen Amurka da Birtaniya ke yi, domin hana daukar duk wasu matakai na shari'a da adalci a kan Isra'ila.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da mataimakin babban sakataren gamayyar kungiyoyin lauyoyi larabawa Abdulazim Almagribi, ya bayyana cewa : babbar matasalar da ake fuskanta wajen gurfanar da Haramtacciyar Kasar Isra'ila a gaban kuliya ita ce hawa kujerar naki da kasashen Amurka da Birtaniya ke yi, domin hana daukar duk wasu matakai na shari'a da adalci a kan Isra'ila. Ya ci gaba da cewa gamayyar kungiyoyin lauyoyi larabawa ta bi hanyoyi da dama domin hukunta Isra'ila kan ayyukan yaki da ta tafka kan al'ummar Palastinu, hakan kuwa ya hada da bi ta hanyar kotunan kasashen Spain, Belgium, Birtaniya, Canada da dai sauransu, amma babbar matasalar da suke fuskanta ita ce gwamnatocin kasashen Amurka da Birtaniya sun sha alwashin kawo cikas ga duk wani yunkurin gurfanar da Isra'ila a gaban kuliya sakamakon ayyukan yaki da ta tafka kan al'ummar Gaza. ya ce yanzu haka akwai kungiyoyi kimanin 500 masu zaman kansu da suka hada kai da su domin ganin an kai Isra'ila kotun manyan laifuka ta duniya.
393553