IQNA

Shugaban Kasar Iran Ya Isar Da Sakon Musulunci A Taron Jenneva

17:14 - April 26, 2009
Lambar Labari: 1770096
Bnagaren siyasa: Abin da ke cikin zukatan al'ummomin Iran palastinu da Labanan da ma sauran kasashen musulmi ne shgaban kasar Iran ya isar a cikin kalma guda a taron birnin Jenneva.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya habarta cewa, babban malamin lardin Khurasan Sayyid Qasim Ya'akubi, ya bayyana cewa abin da ke cikin zukatan al'ummomin Iran palastinu da Labanan da ma sauran kasashen musulmi ne shgaban kasar Iran ya isar a cikin kalma guda a taron birnin Jenneva. Ya ci gaba da cewa shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad ya bayyana wa sauran al'ummomin duniya irin gwarzantakar da ya koya daga juyin juya halin musulunci na Iran, ya ce babban abin da ke ci ma al'ummomin duniya tuwo a kwarya musamman ma na musulmi, shi abin da ya yi tsokaci a kansa a wajen taron yaki nuna wariya na majalisar dinkin duniya da aka gudanar a birnin Jenneva na kasar Switzerland, lamarin a cewarsa kasashe masu girman da ke marawa Haramcciyar kasar Isra'ila baya neb a su ji dadinsa ba.


393909
captcha