IQNA

Babbar Mafita A Wurin Musulmi Ita Ce samun Hadin Kai Tsakaninsu

17:13 - April 26, 2009
Lambar Labari: 1770099
Bangaren siyasa da zamantakewa: limamin juma'a a birnin Bahar da ke cikin Iran ya bayyana cewa hadin kai tsakanin al'ummar Musulmi shi ne hanyar warware matsaloli da dama da duniyar musulunci ke fuskanta a halin yanzu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; : limamin juma'a a birnin Bahar da ke cikin Iran ya bayyana cewa hadin kai tsakanin al'ummar Musulmi shi ne hanyar warware matsaloli da dama da duniyar musulunci ke fuskanta a halin yanzu. Ya ci gaba da cewa jamhuriyar musulunci ta Iran tana taka gagarumar rawa wajen hada kan al'ummar musulmi domin ta hakan ne kawai za su iya cimma burinsu, ya ce hada kan al'ummar musulmi na duniya na daya daga cikin muhimman manufofin juyin juya halin musulunci a Iran. A bangare guda kuma ya tabo batun kai hare-haren ta'addancin da aka yi kan musulmi masu kai ziyara a wurare masu tsarki da ke kasar Iraki da suk ahada mutanen Iran, inda wasu daga cikinsu suka yi shahada wasu kuma suka samu raunuka, ya ce duka wannan yunkuri ne na kawo rarraba tsakanin musulmi, kuma dole ne musulmi su yi hattara.


394035

captcha