IQNA

Kungiyar OIC Ta Yi Allawadai Da Harin Kazimiyyah

13:57 - April 27, 2009
Lambar Labari: 1770572
Bangaren kasa da kasa: Kungiyar hadin kan musulmi ta OIC ta yi Allawadai da harin ta'addancin da aka kai kan masu ziyarar hubbaren Imam Musa Kazim (AS) da ke Kazimiyya a kasar Iraki, lamarin da ya yi sanadiyar yin shahadar mutane fararen hula da dama.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait KUNA cewa; A cikin wani bayani da ta fitar kungiyar hadin kan musulmi ta OIC ta yi Allawadai da harin ta'addancin da aka kai kan masu ziyarar hubbaren Imam Musa Kazim (AS) da ke Kazimiyya a kasar Iraki, lamarin da ya yi sanadiyar yin shahadar mutane fararen hula da dama. Bayanin ya ci gaba da cewababu wani dalili a cikin wane addini da ya bayar da dama zubar da jinin fararen hula ba gaira ba sabar, balantana addinin muslunci, wanda addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai. A nata bangaren cibiyar kula da harkokin ilimi da yada al'adun addinin musulunci ta ISESCO ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta yi Allawadai da kai wannan hari na ta'addanci a Kamzimiyyah.

394552

captcha