IQNA

Siyasar Kwamitin Tsaro Ce Ta Hana Binciken Laifukan Isra'ila

14:03 - April 27, 2009
Lambar Labari: 1770578
Bnagaren kasa da kasa: Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya matsayinsa na babbar madogara wajen kare hakkin al'ummomin duniya tare da tabbatar da tsaronsu, shi ne ya koma kare siyasar zalunci da danniyar Isra'ila kan al'ummar palastinu, tare da hana bincika laifukan yaki da take aikatawa kan fararen hula ta hanyar hawa kujerar naki.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da wani malamin jami'a a bangaren shari'a kuma alkali a jami'ar Beirut ta kasar Labanan Professor Wasim Mansur ya bayyana cewa; Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya matsayinsa na babbar madogara wajen kare hakkin al'ummomin duniya tare da tabbatar da tsaronsu, shi ne ya koma kare siyasar zalunci da danniyar Isra'ila kan al'ummar palastinu, tare da hana bincika laifukan yaki da take aikatawa kan fararen hula ta hanyar hawa kujerar naki. Ya ci gaba da cewa babban abin mamaki ne yadda kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya ki yin Allawadai da ayyukan ta'addancin da Isra'ila take aikatawa kan al'ummar palastinu, ya ce a wasu lokuta da suka gabata majalisar dinkin duniya ta bayyana Isra'ila a matsayin daula ta nuna wariya, kuma ta yi Allawadai da tsarin danniya na Isra'ila, amma kuma yanzu majalisar ta janye wannan kudiri.


394021
captcha