Daga Labanon ne Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoto cewa: fadllah a cikin wannan bayani ya bayyana cewa: yin Allah wadai da tofin Allah tsine kan harin baya-bayan nan a Iraki gay an ta'adda bai wadatar ba sai malummai na addini da kungiyoyin musulmi sun yi wani abu a aikace da zai hana abkuwar irin wannan lamari na ta'addanci. Har ila yau a cikin wannan bayani y ace kisan gilla kan fararen hula wadanda bas u san hawa balantana sabka ba a harin kunar bakin wake na ta'addanci da ya yi sanadiyar shahada da jikkata da dama daga cikin fararen hula.
394559