Bangaren siyasa da zamantakewa; wani gungu na masu fitar da fatawa a kasar Labanon sun sun halarci taron kasa da kasa na masu fitar da fatawa a duniya karo na sha tara.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna ce ta watsa labarin cewa: Muhammad Rashid Kabani mai bada fatawa na kasar Labanon da Khalil Almis mai bada fatawa na yankin Zulha da kuma Khaldun Arimat mai bada fatawa na yankin Baka'a suna daga cikin masu fitar da fatawa na kasar Labanon da suka halarci taron hadin guiwar masu fitar da fatawa na kasa da kasa karo na sha tara da aka gudanar a hadaddiyar daular larabawa.
395408