IQNA

An Kawo Karshen Gasar Karatun Kur'ani Ta Makarantun Trabulus A Kasar Labanon

15:46 - April 28, 2009
Lambar Labari: 1771217
Bangaren kula da harkokin Kur'ani : An kawo karshen gasar karatun kur'ani karo na talati na makarantun yankin Trabulus na kasar Labanon.
Daga Labanon ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; a wannan gasar karatun kur'ani an samu halartat mahardata 1200 yan makaranta mata da maza da kuma wasu yan takara mahardata 135 yan koleji da kuma gaba da haka da suka fito daga yankuna daban daban na arewacin kasar ta Labanon .Wannan karo an samu halartar mahardata masu yawan gasket a wannan gasar karatun kur'ani ne suka samu damar shiga da hakan ke nuni da yadda mutane suka yi maraba da wannan gasar da karbuwa a gare su.

395371

captcha