IQNA

Wakilan Al'umma A Aikace Yaya Suke Yin Tattali Ga Al'umma

Bangaren manema labarai: Wakilin Jagora a yankin azarbaijan ta gabas kuma limamin masallacin juma'a na Tabriz ya bayyana cewa; dole shugabanni su kasance abin koyi ga al'umma da dogaro ta fuskar yin tattali da hana almubazziranci.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: Ayatullah Muhsin Mujtahid Sahbsatari wakilin jagora a yankin azarbaijan ta gabas kuma limamin juma'ar Tabriz ya yi nuni da bayanan jagoran juyin juya halin musulunci na Iran kan aiwatar da tattali da hana almubazzitranci a aikace da zama abin koyi ga jama'a a wani taron komitin al'adu da cewa babban wanda ake nufi da nuna yatsa kan sa kan wannan jawabi na jagora sun e shugabanni da wakilan al'umma da kuma sune yafi dacewa su fara aiwatar da wannan lamari a tsakanin al'umma da zama abin koyi ga saura.

395036