IQNA

Dakin Karatu Na Jami'ar Mostafa Da Ke Mashhad A Duniya Irinsa Ya Yi Karanci

Babban dakin karatu na jami'ar Mostafa reshenta da ke birnin Mashhad daya ne daga cikin manyan dakunan karatu da suka yi karanci a duniyar musulmi, duk da cewa dakin karatu na Imam AS ya yi kama da shi, inda yake da littafai sama da dubu saba'in da biyar.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da daya daga shugabannin jmai'ar Mostafa reshen Mashhad Hasan Akhlaqi Amiri, ya bayyana cewa; dakin karatu na jami'ar Mostafa reshenta da ke birnin Mashhad daya ne daga cikin manyan dakunan karatu da suka yi karanci a duniyar musulmi, duk da cewa dakin karatu na Imam AS ya yi kama da shi, inda yake da littafai sama da dubu saba'in da biyar. Ya ci gaba da cewa yanzu haka an tanadi littafai a cikinsa masu dimbin yawa, wadanda masu bincike za su iya yin amfani da su wajen gudanar da bincike, ya ce adadin liffatan da ke cikinsa a halin yanzu sun tasamma dubu casa'in, daga cikin littafan kuwa akwai na larabci da na turanci gami da na harshen farisanci


395537