IQNA

An Gano Kusakurai A Cikin Rubutun Kur'ani Bugun Demacus

15:59 - April 28, 2009
Lambar Labari: 1771232
Bangaren al'adu da zamantakewa: wasu malamai a kasar saudiyya sun gano wasu kurakurai a cikin rubutun kur'ani bugun birnin Demacus na kasar Syria.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Moslim cewa; daya daga cikin malaman kur'ani na kasar Saudiya Mohammad Nahari ya bayyana cewa, sun samu wasu kurakurai a cikin wani kur'ani bugun birnin Demascus, amma kurakuran daga na'urar buga haruffan kur'anin ne, kamar a cikin wani da aka samu na'aurar ba ta buga sunayen ubangiji wato sunan jalalah, a cikin wasu shafukan kuma na'urar ba ta buga haruffa da suka hadu da harafin mim a karshe. Bayan fahimtar hakan an mika kur'ani ga bangaren da ke kula da harkokin adini da kratun kur'ani na kasar domin tabbatar da kurakuran kafin fadakar madaba'antar da ta buga kur'ani domin sake dubawa. Ya ce yara 'yan makaranta da ke karatun kur'ani ne suka gano kurakuran da ke cikin wannan kur'ani, wanda madaba'antar Darul kur'an ta birnin Demascus ta buga.

395466



captcha