Bangare kasa da kasa: Wasu daga musakai daga nahiyar za su kai wata ziyara zuwa zuwa Zirin Gaza, domin nuna goyon bayansu ga al'ummar yankin musamman ma wadanda suka samu raunuka da suka nakasa su a hare-haren ta'addancin da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan a'ummar yankin a 'yan lokutan baya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Palestine-info cewa, daya daga cikin masu shirya ziyarar musakai na nahiyar turai ya fadi cewa; Wasu daga musakai daga nahiyar za su kai wata ziyara zuwa zuwa Zirin Gaza, domin nuna goyon bayansu ga al'ummar yankin musamman ma wadanda suka samu raunuka da suka nakasa su a hare-haren ta'addancin da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan a'ummar yankin a 'yan lokutan baya. Ya ci gaba da cewa bababr manufar ziyarar ita ce ganewa idanunsu halin marassa lafiya ke ciki domin kai musu taimako, tare da karfafa gwiwarsu dangane da mawuyacin halin da aka jefa su ciki, ya ce yanzu haka mutane da dama da suke bukatar su kasance cikin wannan tawaga zuwa Gaza daga nahiyar turai.
395513