IQNA

An Yada Littafin Muhammad Manzon Allah A Cikin Harshen Gyrgystan

Bangaren ilimi da fikira: Littafin nan mai suna Muhammad SAW manzon Allah ne an fassara shi a cikin harshen Gyrgystan tare da buga shi da ma yada shi a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Gyrgystan ya habarta cewa; littafin nan da aka rubuta a cikin harshen larabci mai suna Muhammad SAW manzon Allah ne an fassara shi a cikin harshen Gyrgystan tare da buga shi da ma yada shi a kasar. Wannan littafi dai ya kunshi tarihin manzon Allah Muhammad ne tun daga rayuwarsa ta kuruciya har zuwa lokacin da ya karbi manzonci. Littafin wanda aka buga a cikin shafuka 350 yanzu haka dai ya shiga kasuwa ana sayar da shi a sassa daban-daban na kasar. Littafin dai ya warware da dama daga cikin karairaki da aka danganta su da addinin Musulunci musamman ma manzon Allah SAW da nufin bakanta surarsa a idon sauran al'ummomin duniya mabiya wasu addinai na daban.

392436