IQNA

Musulmin Thailand Na Nuna Goyon Baya Ga Al'ummar Palastine

Bangaren siyasa da zamantakewa: Musulmin kasar Thailand na ci gaba da nuna goyon bayansu ga al'ummar palastinu tare nuna kiyayyarsu ga ayyukan zalunci da danniya na Haramtacciyar Kasar Isra'ila kan palastinawa da ta mamaye wa wurare.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Al'ummar musulmin kasar Thailand na ci gaba da nuna goyon bayansu ga al'ummar palastinu tare nuna kiyayyarsu ga ayyukan zalunci da danniya na Haramtacciyar Kasar Isra'ila kan palastinawa da ta mamaye wa wurare. Rahoton ya ci gaba da cewadaga cikin hanyoyin da musulmin kasar ta Thailand ke bi wajen nuna goyon bayansu ga al'ummar Palastinu, har da gudanar da taruka domin gabatar da jawabai kan muhimmancin palastinu wajen al'ummar musulmi da kuma wurare masu tsarki da ke yanki, da kuma halin kaka ni ka yi da yahudawan sahyuniya suka jefa al'ummar yankin. Ba'ada bayan haka kuma sukan dunka jakuna na hannu da ke dauke zane-zanen nuna goyon baya ga palastinawa da nuna kiyayya ga zaluncin yahudawan sahyuniya.

392730