IQNA

A Ta'addancin Isra'ila A Qods Bai Kawo karshen Dokokin Kasa Da Kasa Ba

13:38 - April 29, 2009
Lambar Labari: 1771664
Bangaren kasa da kasa: Sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa ya bayyana cewa abin da Isra'ila ke yi a Qods ya saba wa dukkanin dokoki na kasa da kasa, kuma hakan ba zai iya kawo karshen dokoki na kasa da kasa ba kamar yadda yahudawa suke zato.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin internet na Qods Press cewa; Amr Musa babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa ya bayyana cewa abin da Isra'ila ke yi a Qods ya saba wa dukkanin dokoki na kasa da kasa, kuma hakan ba zai iya kawo karshen dokoki na kasa da kasa ba kamar yadda yahudawa suke zato. Amr musa ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake zantawa da wata tawagar kasar Spain a birnin Alkahira na kasar Masar, ya ci gaba da cewa muna kara jaddada wa duniya cewa abin da Isra'ila take yi a Qods wuce gonad a iri ne da ya kamata ya kawo karshe cikin gaggawa. Kowa ya ga yadda Isra'ila take cin zarafin dan adam da kuma wulakanta wurare masu tsarki da dukkanin addinai suke girmamawa.

396166


captcha