IQNA

Nigeria Ce Ta Daya Wajen Yawan Mahardata Kur'ani A Duniya.

13:34 - April 29, 2009
Lambar Labari: 1771670
Bangaren kasa da kasa: Shugaban kwamitin malamai na jahar Kano a tarayyar Nigeria ya bayyana cewa; bisa tabbatattun bayanai Nigeria ita ce kasar da tafi kowace kasa yawan mahardata kur'ani a duniya, mafi yawansu kuma mazauna Kano ne.
Kamfanin dillancin labaran Ikan ya nakalto daga shafin internet na Allafrica cewa; Sheikh Ibrahim Khalil a wata ganawa da ya yi da shugaban kwamitin mahardata kur'ani na Nigeria ya bayyana cewa; samun mahardata masu yawa a cikin wannan kasa wata kyauta ce daga ubangiji, amma a bin ban-takaici shi ne yadda kula da lamari yadda ya kamata. Ibarahim Khalil ya kirayi mutanen Nigeria da su ci gaba da kula da kur'ani ba sai ci watan azumi ba kawai, ya ce yanzu haka ana tattaunawa tare da bangaren gwamnati domin bayar da digirin digigir ga mahardata kur'ani.

396145
captcha