IQNA

An Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani A Kasar Turkiya

13:37 - April 29, 2009
Lambar Labari: 1771677
Bangaren kasa da kasa: An gudanar da gasar karatun kur'ani ta 'yan makarantar sakandare a kasar Turkiya, wanda bangaren kula da harkokin addini na ma'aikatar ilimi ta kasar ya dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ma'aikatar kula harkokin ilimi ta kasar Turkiya cewa; An gudanar da gasar karatun kur'ani ta 'yan makarantar sakandare a kasar Turkiya, wanda bangaren kula da harkokin addini na ma'aikatar ilimi ta kasar ya dauki nauyin shiryawa da gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa wadanda suka shiga cikin gasar dukkaninsu yara ne matasa masu karatun islamiyya a matsayi na gaba da firamare, kafin wannan lokacin an fara gudanar da gasar a mataki na share fage, inda a jiya aka gudanar da mataki na nkarshe, wanda da shi ne aka kawo karshen gasar. Za a ci gaba da gudanar dawannan gasa ta karatun kur'ani kowace shekara kamar yadda aka yi a shekarun baya.

396094

captcha