IQNA

Ofishin Kula da Al'adun Iran A Tailand Ya Ziyarci Mu'assisar Kur'ani Ta Rasulul A'azam

20:37 - April 30, 2009
Lambar Labari: 1772069
Bangaren al'adu da zamantakewa: Jalal Tamla mai kula da ofishin yada al'adun Iran a Tailand ya ziyarci mu'assisar kur'ani ta rasulul Akram da ke karkashin jami'ar Almustapha(SWA) al'alami.
Daga kudu maso gabacin Asiya ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: a wannan ziyara ta nuna kauna da kusanci da juna ce inda bayan karatun kur'ani mai tsarki hujjatul islam Amiri wakilin jami'ar Almustapha (SWA) Al'alami a Tailand ya yiwa mai kula da ofishin yada al'adun Iran a wannan kasa maraba da zuwa da cewa: bayan gabatar da ma'aikatan wannan mu'assisa ta Rasulul Akram (SWA) ya gabatar da rahoto kan ayyukan da suke gudanarwa a takaice.Shi ma mai kula da ofishin yada al'adun Iran a wannan kasa ya yaba da wannan jan kokari nasu da jinjina masu matuka gaya.

39613713

captcha