Bangaren kasa da kasa: Za a bayar da horo ga alkalan gasar kur'ani a kasar Saudiyya a karo na uku, wanda cibiyar kula da harkokin addinin mulunci da yada al'adunsa ta kasar ta dauki nauyin shiryawa a birnin Riyad fadar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Almadina da ake bugawa a kasar Saudiyya cewa; za a bayar da horo ga alkalan gasar kur'ani a kasar Saudiyya a karo na uku, wanda cibiyar kula da harkokin addinin mulunci da yada al'adunsa ta kasar ta dauki nauyin shiryawa a birnin Riyad fadar mulkin kasar. Rahoton ya ci gaba da cewa alkalai 16 ne za su samu wannan horo da suka hada da mata 10 gami da maza 6. Daga cikin muhimman abubuwan da za su koya a wajen horon kuwa har da yadda za su gudanar da alkalanci kan matsayin harda da kuma karatu, da kuma hanyoyin gano kuskure cikin sauri, da kuma fadakar da mai karatu cikin hanya ta ruwan sanyi ba tare da an ruda shi ba.
396832