IQNA

OIC Ta Yi Suka Kan Yada Wasannin Computer Masu Yin Tozarci Ga Addinai

20:32 - April 30, 2009
Lambar Labari: 1772077
Bangaren kasa da kasa: Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka dangane da fitar da wasu wasannin na'ura mai kwakwalwa da ake yi domin cin zarafin wasu addinai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin Internet na OIC cewa; Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka dangane da fitar da wasu wasannin na'ura mai kwakwalwa da ake yi domin cin zarafin wasu addinai. Ofishin kungiyar da ke birnin Jidda na kasar Saudiyya ne ya sanar da hakan a cikin wani bayani day a fitar jiya, inda ya bayyana wadannan ayyuka da cewa ayyuka na tozarta addinan muslunci da kiristanci wadanda aka safkar daga sama, da nufin kawo wani sabon rikici tsakanin mabiya addinai daban-daban a fadin duniya. Bayanin ya ce wajibi ne day a rataya kan bangarorin da suke harhada wasanni a cikin na'ura mai kwakwalwa da su kaucewa aikata duk wani abin da zai kawo rikici tsakanin mabiya addinai.

396724




captcha