IQNA

An Gudanar Da Wani Taro Domin Girmama Ma'aiki SAW A Birnin London

20:31 - April 30, 2009
Lambar Labari: 1772079
Bnagaren kasa da kasa: An gudanar da wani zama a birnin London na kasar Birtaniya domin girmama manzon Allah SAW, wanda kungiyar matasa musulmi na birnin Anatoli suka shirya a babbar cibiyar yada al'adu ta Frieds house da ke birnin London.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Zaman ta kasar Turkiya cewa; An gudanar da wani zama a birnin London na kasar Birtaniya domin girmama manzon Allah SAW, wanda kungiyar matasa musulmi na birnin Anatoli suka shirya a babbar cibiyar yada al'adu ta Frieds house da ke birnin London.
Bayanin ya ci gaba da cewa a yayin bude taron an gabatar da karatun kur'ani mai tsarki, daga cikin mahalarta taron akwai malamai da marubuta gami da musulmin kasar Birtaniya daga birane daban-daban na kasar. Babbar manufar gabatar da taron dai ita ce kara wayar da kan musulmi da ma wadanda ba musulmi dangane da matsayin ma'aiki da kuma sakon da ya zo da shi na musulunci, tare da mayar da martini ga masu sukar addinin musulunci tare da bayyana shi da cewa addini ne na tashin hankali.


396750


captcha