IQNA

Kwamitin Kashe Masu Magana Da Turkanci Zai Gudanar Da Zama A Istanbul

19:09 - May 02, 2009
Lambar Labari: 1772864
Bnagaren gasa da kasa: Majalisar musulmi ta kasashe masu Magana da harshen Turkanci za ta gudanar da zamanta a birnin Istanbul na kasar turkiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na bangaren da ke kula harkokin addinin musulunci a kasar Turkiya cewa; Majalisar musulmi ta kasashe masu Magana da harshen Turkanci za ta gudanar da zamanta a birnin Istanbul na kasar Turkiya. Bayanin yab ci gaba da cewa wannan shi ne karo na bakwai da za a gudanar da wannan zaman taro, wanda zai samu halartar malamai da masana daga kasashe masu Magana da harshen Turkanci, da kuma wasu daga cikin shugabannin musulmi daga kasashe daban-daban na nahiyar Asia. A zaman taron za a saurari shawarwari daga dukkanin wadanda aka gayyata zuwa ga zaman taron, dangane da muhimman abubuwan da ya kamata a saka a gaba domin ci gaban addinin musulunci.

397549
captcha