Bnagaren kasa da kasa: Shirin nan da cibiyar musulmin kasar kasar Amurka ta bullo da shi na yada ilmomin kur'ani ta hanyar internet ya samu karbuwa matuka
Kmafanin dillancin labaran Ikna yanakalto daga shafin internet na cibiyar ilimi ta musulmi Washingto cewa; Shirin nan da cibiyar musulmin kasar kasar Amurka ta bullo da shi na yada ilmomin kur'ani ta hanyar internet ya samu karbuwa matuka. An kirkiro shirin ne tun shekarar da ta gabata, a daidai lokacin da ake tunawa da lokacin shahadar Allamah Mottahari, da nufin raya ilmomin kur'ani tsakanin al'ummar musulmi. Daga cikin shirye-shiryen da ake ayadawa a cikin wannan shafi hard a karatun kur'ani daga makaranta da suka yi fice a duniyar musulmi. A cikin watan Ramadan da ya gabata akan saka karatun kur'ani a kowace rana , inda ake safke kur'ania kowace rana daga cikin ranakun watan Ramadan, inda makaranta kur'ani kan shiga kai tsaye domin bayar da tasu gudunmawa.
397671