Bnagaren kasa da kasa: Babbar majalisar musulmin Qods ta yi Alladawai da gina majami'ar yahudawan sahyuniya da Isra'ila ke ci gaba da yi yanzu haka a gefen masallacin Qods mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana cewa; Babbar majalisar musulmin Qods ta yi Alladawai da gina majami'ar yahudawan sahyuniya da Isra'ila ke ci gaba da yi yanzu haka a gefen masallacin Qods mai alfarma. A cikin wani bayani da ta fitar, majalisar musulmi Qods ta bayyana cewa abin da Isra'ila ta ke aikatawa na tozarta wurare masu tsarki da alfarma da dukkanin mabiya addinai da aka safkar daga sama, ya saba wa dukkanin dokoki na kasa da kasa. Yanzu haka dai Isra'ila na ci gaba da gina wata babbar majami'ar yahudawan sahyuniya, wadda ita ce majami'a mafi girma a birnin Qods, wadda za a kasha kudi sama da dalar amurka miliyan arba'in wajen gina ta.
397714