Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alkhalij cewa; kwamitin kula da gasar kur'ani ta kasa da kasa zai jagoranci gudanar da gasar karatun kur'ani a birnin Dubai. Shugaban kwamitin kula da harkokin gasar karatun kur'ani na kasa da kasa Ibrahim Muhammad Bu Milha ya bayyana cewa; wannan shi ne karo na uku da za a gudanar da wannan gasa da aka yi wa lakabi da mafi kyawun sautin karatun kur'ani da kira'ar tartili, kumsa za a kwashe kwanaki biyar a jere ana gudanar da wannan gasa, wadda za ta samu halartar fitattun makaranta kur'ani daga sassa daban-daban na hadaddiyar daular larabawa.
397902