Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet ma'a cewa; An gudanar da taron gasar hardar kur'ani mai tsarki a zirin Gaza, wanda ya samu halartar dalibai daga sassa daban-daban na zirin Gaza. Shugaban bangaren da ke kula da harkokin gasar kur'ani a yankunan zirin Gaza Nasruddin Madukh ya bayyana cewa, babbar manufar gudanar da gasar ita ce karfafa gwiwar matasa wajen shiga cikin harkokin karatun kur'ani da hardarsa. Daga cikin wadanda za su shiga cikin gasar har da matasa da shekarunsu ba su wuce takwas zuwa goma sha biyu ba, kamar yadda hardar zata hada da dukkanin kur'ani da kuma rabi gami da rubu'i.
397940