IQNA

Isra'ila Ta Hana Dawo Da Dutsen Nan Na Tarihi A Masallacin Qods

15:13 - May 04, 2009
Lambar Labari: 1773871
Bangaren kasa da kasa: Babbban mai bayar da shawara kan harkokin masallacin Qods Hatam Abdulkadir ya bayyana cewa; Haramtacciyar Isra'ila ta hana dawo da dutsen nan na tarihi da ke cikin masallacin Qods.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alqods da ake bugawa a Palastinu cewa; Babbban mai bayar da shawara kan harkokin masallacin Qods Hatam Abdulkadir ya bayyana cewa; Haramtacciyar Isra'ila ta hana dawo da dutsen nan na tarihi da ke cikin masallacin Qods. Ya ci gaba da cewa tun lokacin da aka dauke dutsen daga wurinsa har inda yau take ba a mayar da shi ba, wanda yahudawan sahyuniya suka ce ba za su taba amincewa da a mayar da dutsen a wurinsa na asali ba, duk da cewa kafin dauke shi sun bayar da tabbaci kan lallai za a dawo da shi wurinsa bayan kammala yin gyare-gyare, amma yanzu yahudawan sahyuniya masu tsattsaran ra'ayi da suka kafa gwamnati sun ki amincewa da hakan.


398219
captcha