Bangaren kasa da kasa: Bankin Musulunci da ke Dubai ya karfafa harkokinsa ta hanyar wayar salula da nufin saukaka kai komo tsakanin masu mu'a'amala da bankin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na AME cewa; Bankin Musulunci da ke Dubai ya karfafa harkokinsa ta hanyar wayar salula da nufin saukaka kai komo tsakanin masu mu'a'amala da bankin.Shugaban bankin Misbah Alkaizi ya bayyana cewa dukkanin masu mu'amala da wannan banki za su iya yin amfani da wayar salula wajen saka ko fitar da kudi daga asusun kudadensu da ke cikin bankin ba tare da wata matsala. Ya ce yin hakan zai taimaka ma masu hada-hada a bankin da ma sauran rassansa da ke wasu kasashe wajen gudanar da harkokinsu, kamar yadda ya bayyana cewa masu mu'amala da bankin za su iya duba shafinsa na internet domin samun cikakken bayani kan hakan.
398294