Bangaren kasa da kasa: Littafin nan mai suna ci gaba a tarihin Musulunci da na larabawa ya samu karbuwa bayan da Isesco ta buga shi tare da yada shi a kasashen duniyar musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran SANA cewa; Littafin nan mai suna ci gaba a tarihin Musulunci da na larabawa ya samu karbuwa bayan da Isesco ta buga shi tare da yada shi a kasashen duniyar musulmi. Yanzu haka dai dai an fara sayar da wannan littafi a wasu manyan shagunan sayar da littafai na kasashen larabawa da na muslmi, inda ya samu karbuwa daga masana kan tarihin Musulunci da ma masu yin nazari kan abubuwan da ke kai da komowa ta fuskacin siyasar addinin addinin Musulunci a duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar fitar da littafin ita ce bayar da masaniya ga wadanda suke bukatar sanin tarihin muslunci ta rawar da ya taka ta fuskacin fasaha.
398358