Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran APS cewa; Abdallah Wad Shugaban kasar Senegal ya bayar da shawarar gudanar da taro na kasa da kasa na malaman addinin musulunci da kuma malaman addinin musulunci na nahiyar Afirka. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a birnin Dakar, inda ya ce da dama daga cikin kasashen musulmi na nahiyar Afirka sun nuna sha'awarsu kan a gudanar da wani taro na malaman addinin musulunci na nahiyar, ya ce shi kuma yana bayar da shawarar a gudanar da taruka biyu ne, daya na malaman addini daga nahiyar Afirka, daya kuma na malaman addinin daga dukkanin kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC. A cikin watan Maris din shekara ta 2008 ne Senegal ta dauki nauyin bakuncin taron kasashen musulmi.
398735