Bangaren kasa da kasa: Manyan kasashe masu girman girman kai da azzaluman duniya ba a shirye suke ba da su su kare hakkokin al'ummar Musulmi ko fatan ganin ci gabansu, maimakon haka suna hankoron ganin sun raunana musulmi ne a dukkanin bangarori.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na almodarresi.com cewa; Babban malamin addinin nan na kasar Iraki Ayatollah Modarresi ya bayyana cewa; Manyan kasashe masu girman girman kai da azzaluman duniya ba a shirye suke ba da su su kare hakkokin al'ummar Musulmi ko fatan ganin ci gabansu, maimakon haka suna hankoron ganin sun raunana musulmi ne a dukkanin bangarori. Shehin malamin ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake ganawa da daruruwan daliban jami'a da kuma malaman jami'oi daban-daban na kasar Iraki a birnin Najaf mai alfarma. Ya ci gaba da cewa mun gani a tsawon tarihi cewa, mumunan tsari yana hana duk wani ci gaban al'umma, kuma hakan na samo asali ne daga munan dokoki da ka'idoji da tsarin ke kafuwa kansu.
398769