Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Ukaz ta kasar Saudiyya cew; Cibiyar kula harkokin sadarwa na marassa rinjaye a kasar Saudiyya za ta gudanar wata gasar karatun kur'ani da al'ummomi marassa rinjaye da ke zaune a kasar ta Saudiyya. Shugaban cibiyar ya bayyana cewa babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce karfafa gwiwar marassa rinjaye a cikin harkokin addinin, da hakan ya hada da batun gasar karatun kur'ani da kuma harda gami da kiyaye ka'idojin karatunsa, ba'ada bayan haka kuma wannan gasa za ta hada dad a bayar da horo na musamman ga matasa maza da mata da nufin ba su kyakkyawan horo wajen sanin ka'idojin karatun kur'ani yadda ya kamata.
398733