Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Cihan cewa; Shugaban kungiyar musulmin kasar Holland Kasim Akadmir ya karbi lambar yabo daga sarkin kasar Holland a wani taro na musamman da sarkin ya kira kan hakan. Sarkin kasar Holland Andry Haridma ya bayar da wannan kyautar girmamawa ga shugaban kungiyar musulmin kasar ne saboda rawar da ya taka wajen kusanto da fahimta tsakanin mabiya addinai daban-daban, domin samun zaman lafiya da fahimtar juna mai dorewa a tsakaninsu. Wani daya daga cikin Musulunci kasar Holland din ya bayyana cewa sarki kasar ba shi da wata matsala da musulmi, kuma ba ya nuna musu kiyayya, maimakon haka ma yana kara kusanto da su ne a cikin dukkanin harkokin kasar.
398642