Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Aljazira da ake bugawa a kasar saudiyya cewa; Za a fara gudanar da gasar hardar kur'ani da tajwidi ta kasa baki daya a birnin Riyad na kasar Saudiyya, wadda za ta kwashe tsawon kwanaki goma jere ana gudanar da ita. Bayanin ya ci gaba da cewa ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar saudiyya ce za ta dauki nauyin gudanar da gasar, wadda yarima Salman bin Abdulaziz zai jagoranci zaman bude ta. A nasa bangaren yarima Salman bin Abdulaziz wanda kuma shi ne magajin garin birnin Riyad ya bayyana cewa; babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce karfafa gwiwar matasa domin su rungumi alkur'ani mai tsarki, ta fuskacin karatu da harda da kuma koyon tajwidi. Gasar zata samu halartar wasu daga cikin jami'an gwamnati.
399259