IQNA

An Fitar Da Wani Fim Kan Addinin Musulunci A Kasar Amurka

Bangaren kasa da kasa : An fitar da wani fim da ke bayyani kan addinin musulunci a yankin Wike Canty da ke cikin jahar Carolina a arewacin kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar The News & Observer cewa; An fitar da wani fim da ke bayyani kan addinin musulunci a yankin Wike Canty da ke cikin jahar Carolina a arewacin kasar Amurka. Rahoton ya ce kungiyoyin musulmi da ke kasar Amurka ne suka fitar da wannan fin din domin wayar da kan al'ummar kasar, dangane da yadda wasu suke ta yada bayanai marassa tushe dangane da addinin musulunci. A cikin 'yan kwanakin nan wasu Amurkawa masu tsananin gaba da addinin musulunci sun tashi kai da fata wajen yada kalamai da bayanai na karya domin kawai su bata sunan addinin musulunci da musulmi a Amurka. A cikin fim din an nuna wani matashi day a fahimci addinin musulunci da kuma dalilan da suka sa shi fahimtar addinin, har ya zama daya daga cikin musulmai.


398968