IQNA

An Fassara Wani Littafi Kan Rayuwar Ma'aiki A Cikin Harshen Turanci

Bangaren Al'adu da fasaha: Littafin nan da Muhammad Reza Sashar ya rubuta dangane da tarihin rayuwar ma'aiki SAW an tarjama shi zuwa harshen turanci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga cibiyar yada al'adu da ilimi ta Darul hadis cewa; : Littafin nan da Muhammad Reza Sashar ya rubuta dangane da tarihin rayuwar ma'aiki SAW an tarjama shi zuwa harshen turanci.Muhammad Reza ya bayyana cewa bisa la'akari da cewa wasu daga cikin wadannan littafai masu matukar muhimmanci an rubuta sun e da harsunan farisanci ko larabci, ya ce lokaci ya yi da musulmi za su tashi tsaye wajen tarjama littafai da dama da aka rubuta kan addinin muslunci da kuma manufofinsa zuwa wasu yaruka, domin ta haka ne kawai za su iya wayar da kan sauran al'ummomi dab a su da cikakkiyar masaniya kan addinin musulunci, domin kuwa abubuwa da dama da ake rubutawa kan addinin musulunci a kasashe dab a na musulmi babu gaskiya a kansu, kuma ana kawar da hankulan al'ummomin kasashen daga addinin musulunci.



399567